1 Jama’ar Ɗan Allah, Ku Taru ku yi murna,
Ku taru, ku taru a Baitalahmi.
Zo mu gaishe shi, Sarkin mala’iku.
Korus:
Mu yi masa sujada, mu yi masa sujada,
Mu yi masa sujada, Mai Centonmu.
2 Zo dai ku gan shi, jariri marar ƙarfi,
Yesu Ɗan Allah ne Madauwami.
Aka haife shi, ba a halicce shi ba. [Korus]
3 Rundunan Sama, yi ta rera waƙa,
Can cikin Sama ku ke yabonsa,
Yabo ga Allah, yabo kuwa ga Ɗansa. [Korus]
4 I, Ubangiji, kai ne mu ke yabo
Gaisuwa mai gaskiya mu ke yi maka.
Kai, Kalmar Allah, cike da alheri. [Korus]
Source: The Cyber Hymnal #14139